Aljeriya: Fiye Da Samarin Afirka 5000 Ne A Cikin Kungiyoyin 'Yan ta'adda.
Shugaban Kasar Aljeriya ya aike da sako ga takwarorinsa na Afirka akan yawan 'ya'yan nahiyar da su ka shiga kungiyar ta'addanci a duniya.
Shugaban Kasar Aljeriya ya aike da sako ga takwarorinsa na Afirka akan yawan 'ya'yan nahiyar da su ka shiga kungiyar ta'addanci a duniya.
A yayin taron da shugabannin kasashen Afirka su ka yi karo na 29 a birnin Adis Ababa na kasar Habasha, Pira ministan kasar Aljeriya, Abdulmajid Tebboune, ya karanta sako a madadin shugaba Butaflika da aciki ya bayyana yadda samarin nahiyar su ke shiga kungiyoyin 'yan ta'adda.
Jawabin shugaban kasar na Aljeriya ya kuma kunshi cewa da akwai kalubale mai yawa a gaban nahiyar saboda yiyuwar dawowar wasu daga cikin 'yan ta'addar.
Shugaba Butaflika ya bukaci ganin an samar da aiki tare a tsakanin kasashen ta fuskar tsaro da tattara bayanai.
A jiya litinin ne dai aka bude taron shugabannin kasashen na nahiyar Afirka karo na 29 wanda ya sami halartar shugabannin kasashen 25.