An Hukunta Misrawa 41 A Kan Laifin Safarar Sassan Jikin Mutum
Lauyen Gwamnatin Masar ya bayyana cewa daga cikin mutane 41 da aka kama da laifin safarar Sassan Jikin Mutum akwai Likitoci da ma'aikatan jiya kuma tuni aka meka su a hannun Kotu
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Lauyen Gwamnatin Masar na cewa bayan gudanar da bincike an gano wani adadi na Likitoci da Ma'aikatan jiya a wata cibiyar kasa da kasa dake safarar sassan jikin Mutum zuwa kasashen waje.
Bisa binciken da aka yi an gano Likitoci 20 da suka kasasnce manbobi a cibiyar dake kula da harakokin ilimi na Jam'i'oi kuma ma'aikata a Asibitocin Gwamnatin kasar, da kuma wasu ma'aikatan jiya guda tara da dilalen sassan jikin zuwa kasashen waje guda 9.
A watan Decembar da ya gabata, Ma'aikatar Lafiyar kasar Masar ta sanar da cewa ta gano babbar cibiyar kasa da kasa ta kasuwancin sassan dan adam a kasar tare da kame mutane 45 da ake zarki da alaka da cibiyar.
Matsalar rayuwa da son ayi kudi a wuri, ya sanya wasu Mutane shiga kasuwancin sassan jikin dan adam a wasu kasashen Duniya