Taho Mu Gama Tsakanin 'Yan Sanda Da Masu Adawa Da Taron G20
(last modified Fri, 07 Jul 2017 11:16:02 GMT )
Jul 07, 2017 11:16 UTC
  • Taho Mu Gama Tsakanin 'Yan Sanda Da Masu Adawa Da Taron G20

Zanga-zangar da Masu adawa da taron G20 a garin Hamburg na Jamus ya yi sandiyar taho mu gana tsakanin su da jami'an 'yan sanda

Dubban masu zanga-zanga ne suka cika tituna, inda suke jifan 'yan sandan kwantar da tarzoma da duwatsu da kuma kwalabe, yayin da 'yan sanda kuma ke harba musu hayaki mai sa hawaye da fesa musu ruwa don tarwatsa su.

Batutuwan da suka shafi kasuwanci da sauyin yanayi da gwajin makamin da Korea ta Arewa ta yi su ne za su mamaye taron na ranar Juma'a da masu sharhi ke ganin za a samu rarrabuwar kawuna a tsakanin shugabannin.

Daya daga cikin abubuwan da za a sanyawa idanu shi ne haduwar keke da keke a karon farko da za a yi tsakanin shugaba Donald Trump da Vladimir Putin na Rasha.

An dai shafe tsawon dare ana bata kashi tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sandan kwantar da tarzoma.

A ranar Juma'a ne kuma ake sa ran kungiyoyin ba da agaji za su yi tasu zanga-zangar, inda za su bukaci shugabannin su kara hobbasa wajen magance matsalar rashin daidaito a tsakanin al'umma.