Ministan Cikin Gidan Kenya Ya Rasu
Gwamnatin Kenya ta sanar da rasuwar ministan cikin gidan kasar, Joseph Nkaissery a wani asibitin dake Nairobi babban birnin kasar.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar yau Asabar ta ce mirigayin dan shekaru 68 a duniya ya rasu ne bayan an kai shi asibitin na Karen domin binciken lafiyarsa.
Gwamanatin dai ta nuna alhininta dangane da rasuwar ministan, saidai bata fayyace lokaci ko kuma sababin mutuwar tasa ba.
A ranar 2 ga watan Disamba na 2014 ne shugaba Uhuru Kenyata ya nada Janar Joseph Nkaissery mai ritaya a matsayin ministan cikin gidan kasar biyo bayan kazamin harin da kungiyar Al'shabab ta dauki alhakin kaiwa a kasar ta Kenya a 2014.
A wani labari na daban daga kasar ta Kenya a kallah mutane tara ne suka rasa rayukansu a wani hari da ake kautata zaton mayakan Al'shabab na Somaliya sun kai a kauyukan Jima da Pandaguo da sanyin safiyar yau Asabar.