Masar Za Ta Binciki Mutuwar 'Yan Kasar Ta A Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22038-masar_za_ta_binciki_mutuwar_'yan_kasar_ta_a_libiya
Ma'aikatar Harakokin wajen Masar ta sanar da cewa za ta gudanar da bincike a kan mutuwar 'yan kasar ta a kasar Libiya
(last modified 2018-08-22T07:00:21+00:00 )
Jul 09, 2017 06:41 UTC
  • Masar Za Ta  Binciki  Mutuwar 'Yan Kasar Ta A Libiya

Ma'aikatar Harakokin wajen Masar ta sanar da cewa za ta gudanar da bincike a kan mutuwar 'yan kasar ta a kasar Libiya

A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Lahadi, Ahmad Abu Zaid mai magana da yawun Ma'aikatar harakokin wajen kasar Masar ya ce daga bangaren wata kungiya dake da alaka da kungiyar bayar da Agajin gaggawa ta kasar Libiya ne suka samu labarin cewa an gano gawawwakin 'yan kasar 19 a yankunan Tabrak da Ajdabiya na arewa maso gabashin kasar.

Kakakin Ma'aikatar Diplomasiyar ta Kasar Masar ya ce ya zuwa yanzu daga cikin gawawwaki 19 an tabbatar  da mutane 7 'yan kasar Masar  tare da kawo gawawwakin gida.

Har ila yau jami'in ya kara da cewa a ganin sa bakin haure ne da suka shiga kasar ba kan ka'ida ba, kuma sun rasa rayukansu ne a hanun masu safarar Mutane.

Tun a shekarar 2011 ne kasar ta Libiya ta fada cikin rikici bayan da Dakarun kungiyar tsaro ta Nato suka kifar da tsohon Shugaban kasar Kanar Mu'amar Kaddafi.