Senegal : An Bude Yakin Neman Zaben 'Yan Majalisar Dokoki
A kasar Senegal an bude yakin neman zaben 'yan majalisar dokokin kasar da za'a gudanarwa a ranar 30 ga watan Yulin nan da muke ciki.
A cewar hukumar zaben kasar mai zamen kanta za'a ci gaba da yakin neman zaben har zuwa ranar 28 ga watan Yuli.
Daga cikin jerin 'yan takara dake neman wakilci a majalisar dokokin kasar har da tsohon shugaba Abdoulaye Wade, da kuma magajin birnin Dakar, Khalifa Sall, dake garkame a gidan kurkuku tun cikin watan Maris bisa zargin karkata akalar kudaden jama'a.
Lauyoyinsa dai sun bukaci kotu ta yi masa sakin talala don ya yi yakin neman zaben.
Yau Litini ne ake sa ran tsohon shugaban kasar Abdulaye Wade mai shekaru 91 zai koma kasar daga Paris domin bude yakin neman zabensa karkashin babbar jam'iyyar adawa ta kasar (PDS).
Mista Wade ya fada a wani gidan talabijin mai zamen kansa na kasar cewa, zai yi yakin namen zabe, amma ba kamar lokacin da yake matashi ba.