Chadi : Ana Adawa Da Goyan Bayan Da Kasashen Yamma Ke Baiwa Deby
(last modified Wed, 12 Jul 2017 05:47:36 GMT )
Jul 12, 2017 05:47 UTC
  • Chadi : Ana Adawa Da Goyan Bayan Da Kasashen Yamma Ke Baiwa Deby

'Yan adawa a Chadi sun kalubalanci goyan bayan da kasashen yamma ke baiwa gwamnatin shugaban kasar Idriss Deby Itmo.

Bangaren matasa na babbar jam'iyyar adawa ta kasar ta aike da wata budaddiyar wasika ga offishin jakadancin kasashen na yamma da dama don nuna damuwarsu kan goyan bayan da kasashensu ke baiwa shugaba Deby.

Offisoshin jakadancin kasashen da bangaren matasan na jam'iyyar ta UNDR ya aikewa wannan wasika sun hada da Faransa, Amurka, Jamus, Switzerland da kuma kungiyar tarayya turai.

Wasikar na kunshe da sakon rashin gamsuwa da goyan bayan da a cewarsu kasashen ke baiwa shugaban da aka zaba ba bisa ka'ida ba.

Tun dai shekara 1990 ne Idriss Deby ke mulki wannan kasa ta Chadi, inda yanzu yake kan wa'adin mulkinsa na biyar.