Senegal : Ba'a Cimma Burin Hana Almajirai Bara Ba
A Senegal, shekara guda bayan kaddamar da shirin nan na hana barace-barace na yara almajirai, kungiyoyi masu zamen kansu sun ce ba'a cimma gurin da ake so ba.
A rahoton da suka fitar jiya kungiyoyin sun ce har yanzu rayuwar almajiran da ake cilastawa yin bara na cikin hadari.
Wani rahoto da hukumar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta fitar ya ce tun daga kaddamar da shirin da gwamnatin Senegal ta yi a Dakar a watan Yuni na bara zuwa watan Maris na 2017 kusan yara almajirai galibi na makarantun allo 1,550 ne aka gano.
A cikin wannan tsarin dai 'yan sanda na kasar sun kaddamar da samame sama da 60 a didajen da ake samun ire iren wadanan yara almajirai, amman duk da hakan lamarin sai kara muni ya ke.
A halin da ake ciki dai kungiyoyin sun bukaci mahukuntan kasar dasu kara zage dantse don shawo kan wannan matsala, duk da cewa wani rahoto da gwamnatin AMurka ta fitar ya nuna cewa gwamnatin Senegal ta yi iya kokarinta, aman ta kara akan hakan.