Najeriya: Harin Kunar Bakin Wake A Maiduguri Ya ci Rayuka Da Dama
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22132-najeriya_harin_kunar_bakin_wake_a_maiduguri_ya_ci_rayuka_da_dama
Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ambato majiyar 'yan sanda na cewa harin da aka kai na kunar bakin wake ne, kuma ya ci rayukan mutane 19 da jikkata wasu 23.
(last modified 2018-08-22T11:30:22+00:00 )
Jul 12, 2017 19:06 UTC
  • Najeriya: Harin Kunar Bakin Wake A Maiduguri Ya ci Rayuka Da Dama

Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ambato majiyar 'yan sanda na cewa harin da aka kai na kunar bakin wake ne, kuma ya ci rayukan mutane 19 da jikkata wasu 23.

Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ambato majiyar 'yan sanda na cewa harin da aka kai na kunar bakin wake ne, kuma ya ci rayukan mutane 19 da jikkata wasu 23.

Kwamishinan 'yan sandan Jahar Borno  Damian Chukwu wanda ya yi magana da manema labaru a wurin da aka kai harin,ya ce mafi yawancin wadanda harin ya rutsa da su, yan kato da gora ne.

Chukwu ya kara da cewa: "Yan kato da gora 12 ne su ka rasa rayukansu, sauran kuma fararen hula.

Shi kuma kakakin 'Yan karo da gora Danbatta Bello ya ce; Sau da yawa yan harin kunar bakin wake su ke kai wa mutanensu hari.