Mali : An Hallaka Wani Kwamandan Mayakan Jihadi
Rahotanni daga Mali na cewa sojojin kasar sun hallaka wani kwamandan mayakan jihadi na kungiyar FLM a tsakiyar kasar.
Kungiyar dake gwagwarmayar kwatar yankin Macina ta (Front de libération du Macina) ta jima tana jagorantar kai hare-haren kan jami'an tsaro.
Wata majiyar soji ta shaidawa kanfanin dillancin labaren AFP cewa wata tawagar sojojin gardi tsarki ne cewa da ''garde national'' sun hallaka dan ta'adda mai suna Bekaye Sangare a yankin Mugna dake nisan kilomita 40 daga yammacin birnin Djenne a jihar Mopti dake tsakiyar kasar.
An hallaka dan ta'addan ne da yammacin jiya Alhamis, a cewar majiyar ba tare da yin karin haske ba kan yadda lamarin ya auku.
Shi dai dan ta'addan Bekaye Sangare, wanda ba'a bayyana shekarunsa ba, shi ne kwamandan kungiyar ta FLM mai alaka da kungiyar mayakan dake ikirari da sunnan addini ta Ansar Dine.