Senegal : Za'a Gudanar Da Bincike Kan Hadari A Filin Kwallo
A Senegal an bude bincike domin gano musababin hadarin da ya yi sanadin mutuwar mutane takwas a wani filin kwallon kafa dake Dakar babban birnin Kasar a ranar Asabar data gabata.
Da yake bayyana hakan a jiya Litini babban mai shiga da kara na gwamnatin kasar, Serigne Basiru Guèye, ya ce bayan aukuwar rikicin da ya yi sanadin mutuwar nan za'a gudanar da bincike domin gurfanar da duk wani mai hannu a rikicin gaban kotu.
Mista Gueye ya ce sun tanadi hotinan bidiyo da bayyanai da dama wadanda ke gaban kotu wandadan za'ayi aiki akansu.
Bayanan da ake dasu dai sun nuna irin laifukan da dama da aka tafka a filin wasan a cewar babban mai shiga da kara na gwamnatin.
A jiya dai an koma yakin neman zamen 'yan majalisar dokoki a kasar, bayan da 'yan takara zaben suka dakatar da kamfe din na tsawan sa'o'i 24 biyo bayan aukuwar lamarin.