Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Duniya Ta Taimakawa Gwamnatin Gambia
(last modified Tue, 18 Jul 2017 12:02:51 GMT )
Jul 18, 2017 12:02 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Duniya Ta Taimakawa Gwamnatin Gambia

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a yammacin Afirka Muhammad Bin Chambas ya bukaci kasashen duniya su ka taimakawa gwamnatin kasar Gambiya

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a yammacin Afirka  Muhammad Bin Chambas ya bukaci kasashen duniya su ka taimakawa gwamnatin kasar Gambiya.

Muhammad Bin Shambas wanda ya gabatar da rahoto a gaban kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya dangane da halin da kasar Gambia ta ke ciki ya ce; Majalisar tana yin aiki tare da kasar ta Gambia don haka tana yin kira ga kasashen duniya da su bada cikakken goyon bayansu ga sauyin siyasar da aka samu a kasar.

Bin Chambas ya kara da cewa; Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar tattalin arziki ta yammacin Afirka ( Ecowas) suna taimakawa gwamnatin Banjul ta fuskokin tsaro da kuma sulhu a tsakanin al'ummar kasar.

Adam Barrow ya hau karagar mulkin kasar ta Gambia ne bayan lashe zabe da kuma tilasta wa Yahya Jameh da ya so yin magudi, sauka da ficewa daga cikin kasar.