An Bukaci Taimakon Gaggawa A Gudancin D/Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22406-an_bukaci_taimakon_gaggawa_a_gudancin_d_congo
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kai agajin gaggawa zuwa Jumhoriyar Demokaradiyar Congo
(last modified 2018-08-22T07:00:25+00:00 )
Jul 20, 2017 01:59 UTC
  • An Bukaci Taimakon Gaggawa A Gudancin D/Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kai agajin gaggawa zuwa Jumhoriyar Demokaradiyar Congo

Gidan Radio na kasa da kasa na kasar Faransa ya nakalto wata kungiyar kai agajin gaggawa na MDD na sanar da cewa cikin watanni shida masu zuwa, 'yan gudun hijra dubu dari da 38 ne ke bukatar taimakon gaggauwa a jihar Paul dake kudancin jumhoriyar Demokaradiyar Congo.

Jihar Paul dai na kan iyaka ne da kasar Congo Brazaville,  sanadiyar hare-haren 'yan tawayen Enzilo, jihar ta fada cikin yanayin rashin tsaro, lamarin da yayi sanadiyar hijra na dubun dubatan fararen hula na yankin.

Tun bayan zaben watan Avrilun 2016 a kasar D/Congo 'yan tawayen Enzilo suka mayar da sansaninsu a yankn na Paul, lamarin da ya yi sanadiyar hijrar fararen hula da dama daga yankin.