Harin Dakarun Tsaron Najeriya A Wuraren 'Yan Ta'addar Boko Haram
Dakarun Tsaron Najeriya Sun fadada kai hare-hare a wuraren mayakan kunigyar Boko haram dake arewa maso gabashin Najeriya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Assabar Rundunar yaki da kungiyar Boko Haram ta sanar da cewa mayakan boko haram da dama suka hallaka a wani farmaki da sojoji suka kai a maboyarsu dake jihar Borno ta shiyar arewa maso gabashin kasar
Sanarwar ta ce farmaki da musaman da Sojojin kasar suka fara kaiwa sun hallaka wasu daga cikin Komondojin kungiyar ta'addancin ta Boko Haram.
Fara kai wannan farmaki na musaman na zuwa ne bayan da Babban hafsan sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya umarci kwamandan rundunonin da ke yaki da Boko Haram a arewa maso gabashin kasar,, Manjo Janar Ibrahim Attahiru da ya kamo shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau a mace ko a raye.
Sanarwar ta ci gaba da cewa janar Tukur Yusuf Buratai na bukatar manjo janar Attahiru ya baza sojojin da ke karkashin ikonsa lungu da sako dan zakulo Shekau a duk inda ya ke boye a Najeriya.
Haka kuma sanarwar ta bukaci 'yan kasar su sanya hannu a wannan gagarumin aiki da ake bukatar yin sa cikin wa'adin kwanaki 40 wajen bayar da duk wata shaida ko karin haske ko wani bayani da zai taimaka wa jami'an tsaro kama jagoran kungiyar.