Sakamakon Zaben 'Yan Majalisun Dokokin Kasar Congo Brazzaville Zagaye Na Farko
A ranar 16 ga wannan wata na Yuli ne aka gudanar da zaben 'yan Majalisun Dokoki da na kananan hukumomin kasar Congo Brazzaville zagaye na farko, sannan ana sa - rai gudanar da zaben zagaye na biyu a ranar 30 ga watan na Yuli domin cike gurbin da suka rage.
A zabukan 'yan Majalisun Dokoki da na kananan hukumomi da aka gudanar a Congo Brazzaville a ranar 16 ga wannan wata na Yuli da muke ciki, jam'iyya mai mulki ta shugaban kasar; Congolese Labour Party (PCT) a takaice ita ce ta samu nasarar lashe mafi yawan kujerun, inda ta samu kujeru 70 daga cikin kujerun 'yan Majalisun Dokokir kasar 151 lamarin da ya bata gagarumar nasara a zagayen farko, yayin da 'yan takarar jam'iyyar mai mulkin su 30 suke da damar sake gwada sa'arsu a zagaye na biyu saboda rashin samun dan takarar da ya samu yawan kuri'un da ake bukata a mazabansa.
Tun a shekara ta 1997 jam'iyyar Congolese Labour Party (PCT) ta shugaban kasar Denis Sassou Nguesso ta dare kan kujerar shugabancin kasar Congo Brazziville tare da samun 'yan Majalisu mafiya rinjaye lamarin da ya bai wa shugaban kasar damar aiwatar da irin ayyukan da ya sanya a gaba. Kamar yadda a bayan zaben shugaban kasa a shekara ta 2016 jam'iyya mai mulki ta "PCT" ta ciga da yin amfani da rinjayenta a Majalisar Dokokin Kasar ta hanyar bai wa shugaban kasar damar gudanar da kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasar.
A bangare guda kuma kasar Congo Brazzaville ta tsunduma cikin rikicin siyasa musamman bayan 'yan watanni kadan da gudanar da zaben shugaban kasa lamarin daya wurga kasar cikin dambaruwar siyasa mai tsanani. Kamar yadda jam'iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula suka sako gwamnatin kasar gaba kan zargin cin zarafin bil-Adama da garkame 'yan siyasa a gidajen kurkuku tare da bayyana cewa gwamnatin Sassou Nguesso tana ci gaba da tsare 'yan adawa a gidajen kurkuku da sunan fada da ayyukan ta'addanci a kasar.
Duk da cewa jam'iyya mai mulki a Congo Brazzaville ta sake kama hanyar samun gagarumar rinjaye a zaben 'yan Majalisun Dokokin Kasar a wannan shekara ma amma duk da haka jam'iyyun adawar kasar musamman babbar jam'iyyar adawa ta Pan-African Union for Social Democracy (UPADS) a takaice ta bayyana cewa: Akwai yiyuwar kawo canji a fagen siyasar kasar Congo Brazaville da ma yankin baki daya. Kamar yadda gwagwarmayar da jam'iyyun siyasar Congo Brazaville gami da na kungiyoyin fararen hulan kasar suke yi zata taimaka gaya wajen cimma bukatunsu kamar yadda tsarin kundin mulkin kasar ya shimfida.