Al'ummar Tunisia Sun Yi Allawadai Da Keta Alfarmar Masallacin Quds
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22512-al'ummar_tunisia_sun_yi_allawadai_da_keta_alfarmar_masallacin_quds
An gudanar da gagarumar zanga-zanga a kasar Tunsia domin nuna goyon baya ga al'ummar palastinu da kuma masallacin Aqsa.
(last modified 2018-08-22T11:30:26+00:00 )
Jul 23, 2017 13:11 UTC
  • Al'ummar Tunisia Sun Yi Allawadai Da Keta Alfarmar Masallacin Quds

An gudanar da gagarumar zanga-zanga a kasar Tunsia domin nuna goyon baya ga al'ummar palastinu da kuma masallacin Aqsa.

Shafin yada labarai na tap cewa, al'ummar Tunisa suna gudanar da jerin gwano a birnin Tunis fadar mulkin kasar Tunisia domin la'antar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila dangane da cin zarafin musulmin Palastinu da kuma keta alfamar wurare masu tsarki.

Tun a cikin shekara ta 1979 ce haramtacciyar kasar Isra'ila ta kwace iko da birnin Quds a hukumance, tare da mayar da masallacin Aqsa ai alfarm a matsayin wani da ke krkashin ikonsu, za su iya hana yin salla a cikinsa a duk lokacin da suka ga dama.