'Yan Sanda Sun Gano Wani Gida Na 'Yan Boko Haram A Kano
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22514-'yan_sanda_sun_gano_wani_gida_na_'yan_boko_haram_a_kano
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta bayyana cewar jami'anta sun gano wani gida a jihar Kano da ake zaton na 'yan kungiyar Boko Haram biyo bayan wani samame da jami'an tsaron suka kai gida a daren jiya Asabar wayewar garin yau Lahadi.
(last modified 2018-08-22T07:00:26+00:00 )
Jul 23, 2017 12:57 UTC
  • 'Yan Sanda Sun Gano Wani Gida Na 'Yan Boko Haram A Kano

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta bayyana cewar jami'anta sun gano wani gida a jihar Kano da ake zaton na 'yan kungiyar Boko Haram biyo bayan wani samame da jami'an tsaron suka kai gida a daren jiya Asabar wayewar garin yau Lahadi.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kanon Rabiu Yusuf ne ya shaida hakan wa manema labarai a yau din nan a Kanon inda  ya ce jami'an nasa sun kai samame kan wannan gida ne da ke yankin Gayawa da ke karamar hukumar Ungogo da misalin karfe biyu na dare bayan  kama wasu mutane da 'yan sandan suka yi wanda hakan ne ya sanya aka kai samame wannan gidan wanda a cewarsa daman jami'an tsaron sun jima suna sanya ido da kuma tattaro bayanan sirri kan wajen.

Kwamishinan ya kara da cewa bayan isarsu gidan ne wadanda suke cikin gidan suka bude musu wuta da kuma jefa musu abubuwan fashewa lamarin da ya sanya 'yan sandan mayar da martani, yana mai cewa daga karshe dai sun sami nasarar kama mutane biyar, uku maza biyu mata da ake tunanin matan wadannan mutanen ne, sai dai ya ce shugaban mutanen wanda wani tsohon soja ne da aka kora ya tsere a daidai lokacin da ake musayen wutan.

Mr. Yusuf ya ce a yayin gumurzun dai wasu 'yan sanda uku sun sami raunuka sannan kuma sun hallaka wasu 'yan Boko Haram din su uku. Kwamishinan ya ce su dai wadannan 'yan Boko Haram din suna daga cikin 'yan kungiyar da aka fatattaka daga dajin Sambisa saboda hare-haren da suka fuskanta daga wajen sojojin Nijeriya a watannin baya.