An Kashe Yan Ta'adda Biyu A Kasar Algeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22570-an_kashe_yan_ta'adda_biyu_a_kasar_algeriya
Majiyar sojojin kasar Libya ta bayyana cewa sojojin kasar sun kashe yan ta'adda guda biyu a yammacin birnin Algies babban birnin kasar .
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jul 25, 2017 10:29 UTC
  • An Kashe Yan Ta'adda Biyu A Kasar Algeriya

Majiyar sojojin kasar Libya ta bayyana cewa sojojin kasar sun kashe yan ta'adda guda biyu a yammacin birnin Algies babban birnin kasar .

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto ma'aikatar tsaron kasar ta Libya tana fadar haka a yau talata, ta kuma kara da cewa sojojin kasar sun kashe yan ta'addan ne a a unguwar Egbal cikin Lardin Tibaje daga yammacin birnin.

Ma'aikatar ta kara da cewa sojojin kasar suna ci gaba neman wasu yan ta'addan a yankin har yanzu. A cikin watanni shida na farkon wannan shekara ta 2017 sojojin kasar Algeria sun kashe yan ta'adda 65 sannan sun kama wasu da ransu. Banda haka akwai wasu mutane 100 wadanda sojojin suke tsare da su a kasar saboda tallafawa yan ta'adda.