Najeriya : An Sace Ma'aikatan Kamfanin NNPC 10
Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu mutane da ake zargi da cewa 'yan Boko haram ne sun sace wasu ma'aikatan kamfanin mai na kasar cewa da NNPC su guda goma a shiyyar arewa maso gabashin kasar.
Wani ma'aikacin kamfanin na NNPC mai suna Ndu Ughamadu, ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa mutanen da aka sace na sashen binciken kimiya ne na jami'ar Maiduguri dake cikin tawagar masu aikin binciken man fetur a yankin .
A cewar Ughamadu tawagar karkashin kamfanin na NNPC na gudanar da aikin binciken man fetur ne a yankin tafkin Chadi, a yayin da mayakan suka sace su a kauyen Jibi dake jihar Borno a arewa maso gabacin kasar.
Bayanai sun ce an gwabza fada tsakanin jami'an tsaro soji dake rakiyar tawagar da kuma mayakan da ake kautata zaton 'yan boko Haram ne kafin su garkuwa da mutanen.
A halin da ake ciki dai an matsa kaimi domin ceto mutanen daga hannun mayakan.