Najeriya: EFCC Ta Kwato Daruruwan Biliyoyin Nairori Daga Kamfanonin Mai
Jul 28, 2017 13:51 UTC
Hukumar yaki da cin hanci da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a najeriya EFCC ta ce ta bankado almundahana da ka yi da makudan kudaden gwamnati a kamfanonin mai na kasar.
Hukumar ta bayyana cewa hakan nea cikin wata sanarwa da kakakinta Wilson Owujaren ya fitar, da ke cewa hukumar ta bi kadun wasu korafe-korafe da aka gabatar mata ne, a kan cewa kamfanonin da suke sayar da man ba su bayar da kudin da ya kamata ga gwamnati ba.
Kudaden dai sun kai kimanin Naira biliyan 329, wadanda aka kwato su a tsakanin watannin Yulin shekara ta 2016 da kuma 2017, duk kuwa da cewa kamfanonin da suke da hannu a cikin almundahanar dai ba su ce komai kan batun ba.
Tags