Wasu 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin 'Yan Sanda A Cote D'ivoire
(last modified Sat, 29 Jul 2017 11:49:54 GMT )
Jul 29, 2017 11:49 UTC
  • Wasu 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin 'Yan Sanda A Cote D'ivoire

Jami'an tsaron cote d'ivoire sun habarta cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda dake kudu maso yammacin kasar.

Kafar watsa labaran Infodrom ta nakalto mahukuntan birnin Fresco na kudu maso yammacin kasar Iviry Coast mai nisan kilomita 180 daga birnin Abidjan na cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda na yankin, inda suka yi musayar wuta tsakaninsu  da jami'an 'yan sandar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dan sanda guda.

Ko baya ga hakan, rahoton ya ce 'yan bindigar sun yi garkuwa da wasu jami'an gwamnati a yankin.

A cewar mhukuntar kasar ta cote d'ivroire, hari da harbe-harben bindiga ya tayar da hankulan mazauna birnin na Fresco, to amma yanzu kwanciyar hankali ya dawo a cikin garin.

A cikin watannin baya-bayan dai kasar ta Cote D'ivoire na fuskantar hare-hare da rikci, inda ko a makun da ya gabata  wasu 'yan bindiga suka kaddamar da hare-hare a kan jami'an 'yan sandar kasar.