Boko Haram Ta Saki Faifan Bidiyon Ma'aikatan Hako Mai Da Ta Sace
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22706-boko_haram_ta_saki_faifan_bidiyon_ma'aikatan_hako_mai_da_ta_sace
Kungiyar Boko Haram ta saki wani bidiyo da ke nuna mutane uku da ta ce ta kama lokacin wani harin kwantan bauna da ta kai wa ma'aikatan hakar mai a jihar Bornon Nijeriya inda daya daga mutanen yake kiran gwamnatin kasar da ta rage amfani da karfi a kan 'yan kungiyar.
(last modified 2018-08-22T07:00:28+00:00 )
Jul 29, 2017 12:32 UTC
  • Boko Haram Ta Saki Faifan Bidiyon Ma'aikatan Hako Mai Da Ta Sace

Kungiyar Boko Haram ta saki wani bidiyo da ke nuna mutane uku da ta ce ta kama lokacin wani harin kwantan bauna da ta kai wa ma'aikatan hakar mai a jihar Bornon Nijeriya inda daya daga mutanen yake kiran gwamnatin kasar da ta rage amfani da karfi a kan 'yan kungiyar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar a cikin faifan bidiyon an nuna mutane ukun zaune inda daya daga cikinsu wanda ya ce shi malamin jami'a ne ya bayyana cewar amfani da karfin tuwo ba shi ne zai magance matsalar ba. Inda ya ce yana kiran gwamnatin tarayyar Nijeriya da ta biya wannan bukata na Boko Haram na daina amfani da karfin tuwo a kansu, su kuma za su sake su.

Har ila yau mutumin ya bukaci mukaddashin shugaban Nijeriyan Prof. Yemi Osinbajo da ya ceci rayuwarsu ta hanyar yarda da bukatar 'yan kungiyar ta Boko Haram wanda yace suna karkashin jagorancin Abu Musab al-Barnawi ne.

A ranar Talatar da ta gabata ce dai 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hari kan wata tawagar ma'aikatan aikin hakar man fetir a jihar Bornon wanda mafi yawansu sun fito ne daga jami'ar Maidguri ne inda suka kashe wasu daga cikin ma'aikatan da wasu sojoji masu musu rakiya bugu da kari kan yin awun gaba da wasu.

Tuni dai mukaddashin shugaban Nijeriyan Yemi Osinbajo ya ba wa manyan hafsoshin sojin Nijeriyan umurnin su koma jiihar Bornon da zama don kara tabbatar da tsaro a jihar biyo bayan hare-haren da 'yan Boko Haram din suke ci gaba da kai wa.