Kungiyar Boko Haram Ta Kai Harin Kunan Bakin Wake A Garin Dikwa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22728-kungiyar_boko_haram_ta_kai_harin_kunan_bakin_wake_a_garin_dikwa
Mayakan kungiyar boko haram sun kai harin kunan bakin wake a garin Dikwa na jihar Borno dake arewa masu gabashin Najeriya.
(last modified 2018-08-22T07:00:28+00:00 )
Jul 30, 2017 07:23 UTC
  • Kungiyar Boko Haram Ta Kai Harin Kunan Bakin Wake A Garin Dikwa

Mayakan kungiyar boko haram sun kai harin kunan bakin wake a garin Dikwa na jihar Borno dake arewa masu gabashin Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto kungiyar bada ajagin gaggauwa ta Najeriya na cewa a daren juma'ar da ta gabata, wani dan kungiyar boko haram ya kai harin kunar bakin wake a garin Dikwa na jihar Borno, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 14 tare da jikkata wasu 24 na daban.

Alkaluma na cewa daga farkon watan yuni zuwa yanzu, hare-haren ta'addancin kungiyar boko haram yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla113.

Tun daga shekarar 2009 ne kungiyar boko haram ta fara kai hare-haren ta'addanci a Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 20 tare da raba wasu sama da miliyan biyu da dubu 300 da mahalin su.