Tashin Bam Yayi Sanadiyar Jikkatar Mutane 10 A Kudancin Somaliya
Wata mota shake da bama-bamai ta tarwatse a garin Kismayo na kudancin kasar somaliya, lamarin da yayi jikkatar mutane 10
A cikin wata sanarwa da jami'an 'yan sanda suka fitar a jiya talata, sun ce motar da aka makire da bamai- bamai ta tarwatse ne a wata babbar hanya mai tsinkoson jama'a, lamarin da yayi sanadiyar jikkata mutane 10 nan take,wasu daga cikin su na ciki mawuyacin hali.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, saidai ana zarkin kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab mai alaka kut da kut da kungiyar Alka'ida da kai harin, ganin cewa ta kwashe shekaru da dama tana kai irin wannan hari na ta'addanci.
Kasar Somaliya dai na daga cikin kasashen Afirka da suke fama da rashin tsaro,lamarin dake kara janyo talauci tare da rashin aikin yi ga matasan kasar.