Iran Za ta ci Gaba Da Kasancewa Tare Da Kasar Syria.
Mai bada shawara ga shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Amir Abdullahiyan ne bayyana haka a yayin ganawa da Pira ministan Syria a birnin Damascus.
Amir Abdullahiyan ya kuma taya gwamnatin Syria murna akan nasarorin da ta ke samu akan 'yan ta'adda da su ka hada da tuddan Arsal da kuma Kalamun ta yamma.
Abdullahiyan ya kuma ce; Yin aiki tare a tsakanin kasashen Iran da Syria yana karfafa matsayar kasashen a cikin yankin gabas ta tsakiya da kuma duniya.
A nashi gefen Pira ministan kasar Syria ya ce; Tun farkon rikicin, gwamnatin Syria ta bukaci ganin an warware matsalar ba tare da an kauce daga kan manufofin kasar ta Syria ba.
Khamis ya yi ishara da cewa yakin da aka damfarawa kasar ta Syria na zalunci ne, sannan ya ce; Karfin kasar yana tattare da hadin kan da ke tsakanin al'umma da kuma hukuma.
Tun a 2011 ne kasar ta Syria ta fada cikin rikici bayan da kasashen turai bisa jagorancin Amurka tare Saudiyya su ka fara aikewa da 'yan ta'adda zuwa kasar da zummar kifar da gwamnatin Basshar Assad.