Ana Zaben Raba Gardama Kan Kundin Tsarin Mulki A Mauritaniya
Aug 05, 2017 05:35 UTC
Yau Asabar ne al'ummar Mauritaniya ke gudanar da zaben raba gardama kan yin gyaran fuskawa kundin tsarin mulkin kasar.
Gyaran dai ya shafi kawo gyara ga tutar kasar, da canza majalisar datijai zuwa ta wakilan jihohi da kuma soke mukamin mai shiga tsakani na jamhuriya da kuma majalisar koli ta addini islama.
'Yan adawan kasar dai sun ce kiran zaben wani yunkuri ne na shugaba Ould Abdel Aziz na yin kwaskwarima ga dokar data kayyade wa'addin mulki biyu.
Daya daga kalubalen dake tattare da zaben na yau shi ne fitowar jama'a a cikin miliyan 1,4 da suka tantanci kada kuri'a, kasancewar 'yan adawan kasar sun bukaci magoya bayansu dasu kauracewa zaben.
Tags