Rwanda : Paul Kagame, Ya Lashe Zabe Da Kashi Sama Da 98%
(last modified Sat, 05 Aug 2017 05:40:00 GMT )
Aug 05, 2017 05:40 UTC
  • Rwanda : Paul Kagame, Ya Lashe Zabe Da Kashi Sama Da 98%

Hukumar zabe a kasar Rwanda ta bayyana shugaban kasar Paul Kagame, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka kada kuri'arsa a jiya Jumma'a.

Hukumar ta NEC mai zaben kanta ta wallafa a cikin daren jiya sakamakon zaben wanda ya shafi kashi 80% na yawan kuri'un da aka kada, wanda ya bayyana Mista Kagame a sahun gaba da kashi 98,66.

Sauran abokan hamayyarsa sun samu ko wanne daga cikinsu kasa da kashi 1% na yawan kuri'un da aka kada, inda dan takara mai zaman kansa, Philippe Mpayimana ya samu kashi 0,72% sai kuma Frank Habineza na jam'iyyar (Parti démocratique vert) wanda ya samu kashi 0,45%.

Wannan nasara ta Paul Kagame bata zo da mamaki ba, tun bayan zaben raba gardama kan kudin tsarin mulikn kasar da aka gudanar a watan Disamba 2015, wanda ya samu amuncewar jama'ar kasar da kashi 98% wanda kuma hakan zai baiwa Mista Kagame wani wa'adin mulki na shekaru 7, da wata killah zai iya bashi damar ci gaba da shugabancin kasar har zuwa shekara 2034.