An Kama Shugaban Babbar Jam'iyyar Adawa A Kasar Chadi
Labaran da suke fitowa daga kasar Chadi sun nuna cewa jami'an tsaron kasar suna tsare da shugaban babbar jam'iyyar adawar kasar mai suna mohammad Adam.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP ya bayyana cewa a safiyar yau Lahadi ne aka kama Mohammad Adam a lokacinda yake kokarin ganawa da dan takarar shugabancin kasar ta Chadi a zaben shekara ta 2016, wanda yake cikin kurkukun Moundou a birnin Njamaina babban birnin kasar.
Kungiyar kare hakkin bil'adama na kasar ta Chadi, har'ila ta bada labarin cewa an kama Mohammad Adam ne tare da wasu yan jam'iyyar adawar kasar wadanda suke kan hanyar zuwa kurkuku don nuna goyon bayansu ga Laokein Medard dan takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2016 da ta gabata, kuma tsohon magajin garin Moudou sai yansanda suka fada masu suka kuma tafi da su.
A ranar 13 ga watan Yulin da ya gabata ne aka kama Laokein Médard tare da zargin yiwa gwamnatin kasar makirci. Ministan tsaron cikin gida na kasar ta chadi ya tabbatar da cewa an kama shugaban jam'iyyar adawar.