Sojojin Sudan Ta Kudu Sun Kwace Babban Sansanin 'Yan Tawayen Kasar
Sojojin kasar Sudan ta Kudu sun kwace babban sansanin 'yan tawayen kasar na Pagak da ke kan iyakan kasar da kasar Ethiopia, lamarin da ya sanya dubun dubatan mutanen gudu da barin wajen.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar sojojin kasar Sudan ta Kudun sun sami nasarar kwace sansanin ne bayan barin wutan da suka yi a wajen lamarin da ya tilasta wa 'yan tawayen gudu su bar wajen.
Har ila yau wasu rahotannin sun jiyo kakakin 'yan tawayen Lam Paul Gabriel yana cewa 'yan tawayen sun ja da baya ne bayan ne daga sansanin na Pagak bayan da suka fuskanci hare-hare ba za ta daga sojojin gwamnatin a safiyar jiya Lahadi, yana mai cewa sun fahimci cewa ci gaba da zama din zai janyo hasara ga fararen hula da kuma sojojinsu don haka su ja da baya.
Shi dai wannan sansani na Pagak tun a shekara ta 2014 ya zamanto wani sansani kana kuma wata helkwatar ayyukan 'yan tawayen Kudancin Sudan din.