An Yau Ne Za A Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Kenya.
An safiyar yau ne za a gudanar da zaben shugaban kasa, 'yan majalisa gami da gwamnoni a kasar Kenya.
Da misalin karfe takwas na safiya yau ne Al'ummar kasar Kenya za su fara kada kuri'insu domin zaben sabon shugaban kasa, 'yan majalisu gami da gwamnonin jihohin kasar, zaben mai cike da fargaba, za a fafata ne tsakanin Shugaban kasar mai ci Uhuru Kenyatta da kuma abokin adawarsa Raila Odinga.
Zaben na yau zai gudana ne cikin wani yanayi, da kwanaki kafin ranar zaben aka kashe daya daga cikin shugabanin kwamitin zaben, lamarin da ya sanya damuwa ga kungoyoyin fararen hula da masu sanya ido kan harakokin zaben na kasa da kasar.
Ko baya ga haka, tun a jiya Litinin Al'ummar birnin Nairobi suka fara kaurace wa birnin don neman mafaka a yankunan bayan-gari a dai-dai lokacin da ya rage kasa da kwana guda a fara kada kuri’a a babban zaben kasar.
A baya-bayan nan ne dai adadin masu fice wa daga birnin na Nairobi ya karu, sakamakon fargabar da wasu ke yi na maimaituwar abin da ya faru a shekarar 2007, in da sama da mutune dubu 1,100 suka rasa rayukansu, yayin da da dama suka kaurace wa gidajensu.
Wannan shi ne karo na biyu da shugaba Uhuru Kenyatta ke tsayawa takara tun bayan darewarsa kan karagar mulki a shekarar 2013, yayin da abokin adawarsa Raila Odinga ya sha kaye har sau biyu a takarar shugabancin kasar a shekarar 2007 da kuma 2013.