Rikici Ya Lashe Rayukan Mutane 34 A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Tashe-tashen hankula suna ci gaba da lashe rayukan mutane a sassa daban daban na Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Hukumar Kula da Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya "OCHA" a rahoton da ta fitar a yau Talata yana dauke da cewa: Bullar tashe-tashen hankula a sassa daban daban na Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya daga ranar 29 ga watan Yulin da ya gabata zuwa ranar 2 ga watan Agustan da muke ciki sun lashe rayukan mutane akalla 34, kuma 14 daga cikinsu fararen hula.
A nata bangaren kungiyar likitoci masu bada agaji kan kiwon lafiya ta Doctor's Without Borders ta sanar da cewa a bayan bullar tashe-tashen hankula a yankin Batangafo da ke arewa maso yammacin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, wasu gungun mahara sun kai farmaki kan sansanin kungiyar ta Doctor's Without Borders.