Al'ummar Sudan Suna Adawa Da Tura Sojojin Kasarsu Zuwa Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23062-al'ummar_sudan_suna_adawa_da_tura_sojojin_kasarsu_zuwa_yemen
Da dama daga cikin mutane da kuma jam'iyyun siyasar kasar Sudan sun ki amincewa da tura sojojin kasar zuwa Yemen domin taya Saudiyya yaki.
(last modified 2018-08-22T07:00:31+00:00 )
Aug 10, 2017 07:57 UTC
  • Al'ummar Sudan Suna Adawa Da Tura Sojojin Kasarsu Zuwa Yemen

Da dama daga cikin mutane da kuma jam'iyyun siyasar kasar Sudan sun ki amincewa da tura sojojin kasar zuwa Yemen domin taya Saudiyya yaki.

A jiya laraba jam'iyyun kasar suka sanar da cewa babu wani alfanu da Sudan za ta samu saboda shiga cikin kawancen larabawa na yaki da kasar Yemen.

Sanarwar ta ci gaba da cewa; Yan kasar Sudan da dama sun rasa raukansu a sanadiyyar yakin, kuma duniya ta yi tir da abinda ya ke faruwa a kasar ta Yemen.

Jam'iyyun Ummah da Kwaminist na daga cikin wadanda su ka yi tir da tura sojojin kasar zuwa yaki a kasar Yemen da shugaba Umar Hassan al-Bashir ya yi.