Rikici Ya Hallaka Mutane 20 A Somaliya
Rikici yayi sanadiyar hallakar mutane 20 a kudu maso yammacin kasar somaliya
Kamfanin dillancin labaran Xin huwa daga birnin magadushu ya habarta cewa rikci tsakanin mayakan kungiyar Ashabab da kuma dakaru masu biyayya da mukhtar Rubu tsohon shugaban kungiyar ta Ashabab yayi sanadiyar mutuwar mutane 20 a kudu maso yammacin kasar.
Rahoton ya ce rikicin ya barke ne a yankin Bakool, kuma an hallaka mayakan Ashabab 15, yayin da bangaren dakarun masu biyayya da tsohon shugaban kungiyar mukhtar Rubu guda biyar ne suka hallaka.
Har ila yau rahoton ya ce da farko mayakan Ashabab ne suka kai harin, inda bangaren tsohon shugaban kungiyar suka samu nasarar dakile shi, lamarin da tilasta mayakan na Ashabab ja da baya.
kafin hakan dai ma'aikatar sadarwa ta kasar somaliyar ta sanar da hallakar Ali muhamad Husain da aka fi sani da Ali Jabal komanda a kungiyar ta Ashabab, kuma shugaban tsarawa da kuma zartarwa na harin bam da kuma kisan gilla, sakamakon farmakin da Dakarun tsaro suka kai a kudancin kasar.