'Yan Adawa Sun Gabatar Da Kudurin Rusa Majalisar Dokokin Afirka Ta Kudu
(last modified Fri, 11 Aug 2017 05:46:02 GMT )
Aug 11, 2017 05:46 UTC
  • 'Yan Adawa Sun Gabatar Da Kudurin Rusa Majalisar Dokokin Afirka Ta Kudu

'Yan adawan kasar Afirka ta Kudu sun gabatar da wani kuduri na rusa majalisar kasar da gudanar da sabon zaben, 'yan kwanaki bayan kayen da suka sha a kokarin da suka yi na tsige shugaban kasar Jacob Zuma.

Rahotanni daga kasar sun bayyana cewar jam'iyyar 'yan adawa ta The Democratic Alliance’s (DA) ce ta gabatar da wannan kudurin a jiya Alhamis tana mai zargin jam'iyyar ANC mai mulki da goyon bayan shugaba Zuman alhali a cewar su al'ummar kasar kuwa ba sa kaunarsa saboda gazawar da ya nuna wajen mulki da kuma rashawa da cin hanci da ake zarginsa da su.

Ana ganin a wannan karon ma da wuya 'yan adawan su ci nasara musamman ganin cewa kudurin na su na bukatar amincewar 'yan majalisa 201 cikin 'yan majalisa 400 da suke majalisar, wanda kuwa jam'iyyar ANC mai mulkin tana da 'yan majalisa 249 a cikinsu.

A kwanakin baya ne dai shugaba Zuman dan shekaru 75 a duniya ya tsallake rijiya da baya a kokarin da 'yan adawan suka yi na tsige shi inda 'yan majalisa 198 suka kada kuri'ar rashin amincewa da shirin tsige shi din alhali wasu 177 kuma suka amince da hakan.