Masar : Hadarin Jiragen Kasa Biyu Ya Yi Ajalin Mutum A kalla 36
Hukumomin kiwon lafiya a Masar sun ce a kalla mutane 36 ne suka rasa rayukansu a yayin da wasu jiragen kasa biyu sukayi taho mu gama a arewacin kasar.
Hadarin wanda ya auku a shigowar birnin Alexandri ya kuma yi sanadin jikatar mutane 109 a cewar Sharif Wadi mukadashin ministan kiwan lafiya a gidan talabijin din kasar.
Wani Hoton bidiyo daga gidan talabijin din kasar ya nuno wani bangare na daya daga cikin jirgin kasan ya jirkice a wata gona inda kuma masu kawo daukin gaggawa ke kwashe mamata da kuma wadanda suka jikkata.
Bayanai daga ma'aikatar kula da sufiri ta kasar sun hadarin ya auku ne bayan da jirgin kasan na farko ya tsaya kan hanya bayan samun matsala, a yayin da jirgin guda ya cikinsa.
Wannan dai shi ne hadarin jirgin kasa mafi muni a wannan kas ata Masar tun bayan wani na watan Nowamba 2013 da ya faru tsakanin motar bas da wani jirgin kasa a kudancin birnin Alkahira wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 27.