Ganawar Buhari Da Tawagar Yada Labaransa A Landan
(last modified Sun, 13 Aug 2017 05:56:59 GMT )
Aug 13, 2017 05:56 UTC
  • Ganawar Buhari Da Tawagar Yada Labaransa A Landan

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, wanda ya shafe sama da watanni uku yana jinya a birnin Landan ya gana da wata tawagar yada labaransa karkashin jagoranci ministan yada labarai da al’adu na kasar Lai Mohamed.

Buhari ya fadi a yayin ganawa da tawagar cewa yana samun sauki sosai, kuma yana son komawa gida amma kuma yana biyaya ne ga umurnin da likitocinsa ke ba shi.

Koda yake babu wata rana takamaimiya da aka bayyana shugaban zai koma gida, amman tawagar data gana da shi ta ce yana samun sauki sosai kuma har yanzu yana cikin raha kamar yadda aka san shi.

kuma sanarwar da tawagar ta fitar bayan ganawa da shi ta ce shugaban na mika godiya ga 'yan kasarsa da sauran kasashen duniya bisa addu'oin samun lafiya da suke ci gaba da yi ma sa.

Tun a ranar 7 ga watan Mayu ne shugaban mai shekaru 74 ya koma birnin Landan domin ci gaba da jinya, saidai har kawo yanzu ba'a bayyana ainahin ciwan dake damunsa ba.

'Yan Najeriya da dama dai na kokonton ko shugaban na da karfi da cikakiyar lafiyar da zai ci gaba da jagorantar wannan kasar.

Ko a 'yan kwanakin da suka gabata gamayar wasu wasu kungiyoyi farar hula sun gudanar da zanga-zanga da zaman dirshin a Abuja fadar gwamnatin kasar domin neman ko shugaban ya koma aiki, ko kuma ya yi murabus saboda halin rashin lafiyar ta sa.

Wannan kuma ya zo ne a daidai lokacin da shugaban ya cika kwanaki casa'in yana jinya a ketare.

Batun cikar shugaba Buhari watanni uku na jinya a ketare ya janjo kace-nace ba kadan ba tsakanin al'ummar kasar, inda wasu ke ganin cewa bai kamata shugaban ya zarta wannan lokacin ba yana waje.

To saidai daga bisani masana tsarin mulkin kasar sun ce babu wani abun damuwa ko tada hankali ko take kundin tsarin mulki, don kuwa shugaba ya mika al'amuran tafiyar da mulki ga mukadashinsa.

Ko baya ga hakan majalisar dattawan kasar ta ce babu wata doka da ta hana shugaban kasa Muhammadu Buhari zama don jinya a ketare har ta sama da watanni uku.

Majalisar wacce ta sanar da hakan a zamanta na ranar Talata data gabata, ta ja hankalin wadanda suka shirya tare da halartar zanga-zanga kiran shugaban ya dawo ko ya yi murabus, da cewa su daina tare da kiran su nisanci rurura rigimar siyasa ba tare da hujjoji ba.

Tsarin mulkin Najeriya dai ya bayyana yadda shugaba ya kamata ya yi a lokuta makamantan wannan, inda ya ce shugaba ya mika ragama ga mataimakinsa ya kuma sanar da majalisun kasar tabatun jinyar, wanda kuwa majalisar ta ce an yi hakan.

Wasu 'yan kasar dai sun ci gaba da bayyana damuwarsu kan yadda shugaban ya ki bayyana a bainar jama'a, wanda wasu ke dangantawa da abin da ya faru lokacin jinyar tsohon shugaban kasar marigayi Umaru Musa 'yar Aduwa, dalilin hakan ne ma ya sa wasu suke ganin bai dace a ci gaba da yin rufa-rufa ba game da halin da shugaba Buhari ke ciki ba.