Jami'an Tsaron Aljeriya Sun Rusa Wasu Maboyar 'Yan Ta'adda Biyu A Kasar
Ma'aikatar tsaron Aljeriya ta sanar da rusa wasu maboyar 'yan ta'adda guda biyu a yankin yammacin birnin Aljes fadar mulkin kasar.
A sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya ta fitar a jiya Litinin ta bayyana cewa: Rundunar sojin Aljeriya ta kai farmaki kan wasu maboyar 'yan ta'adda biyu a yankin Tipaza da ke yammacin birnin Aljes fadar mulkin kasar, inda a maboya ta farko rundunar sojin ta gano bama-bamai masu yawa da na'urori da 'yan ta'addan suke amfani da su wajen aiwatar da ayyukansu na ta'addanci.
Har ila yau a maboyar 'yan ta'addan ta biyu da ke lardin Beji-Muktar; Rundunar sojin ta Aljeriya ta gano manyan bindigogi kimanin 40 da kanana masu tarin yawa. Makobtakar da kasar Aljeriya take yi da kasashen Libiya da Tunusiya da suke fama da ayyukan ta'addanci ya sanya tana fuskantar barazanar ayyukan ta'addancin tare da kwararar 'yan ta'adda cikin kasarta.