Odinga Ya Ce Zai Daukaka Kara Kan Sakamakon Zaben Shugaban Kasar Kenya
Jagoran ‘yan adawar kasar Kenya wanda kuma ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar Raila Odinga ya bayyana cewa zai daukaka kara a kotun koli ta kasar kan sakamakon zaben shugabancin kasar da aka sanar inda shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ya lashe.
Rahotanni daga kasar Kenyan sun bayyana cewar a jiya Laraba ce dai Mr. Odinga ya sanar da wannan aniyar tasa inda ya ce sun yanke shawarar tafiya kotun koli ta kasar don gabatar da kukansu dangane da abin da ya kira 'gagarumin magudin da aka tafka' a yayin zaben shugaban kasar da aka gudanar a makon da ya wuce.
Tun da fari dai Mr. Odinga yayi watsi da kiraye-kirayen da aka yi ta masa na ya daukaka kara kan sakamakon zaben maimakon kiran da yayi wa magoya bayansa na su fito zanga-zanga da yajin aiki, sai dai ya ce a halin yanzu gamayyar jam'iyyun adawa sun tattaro bayanan da suke tabbatar da cewa an yi magudi a zaben.
Tun dai bayan da hukumar zaben kasar Kenyan ta sanar da Uhuru Kenyatta, shugaban kasar Kenyan mai ci, a matsayin wanda ya lashe zaben ne dai Mr. Odinga yayi watsi da sakamakon zaben duk kuwa da bayanan da masu sa ido na kasa da kasa suka fitar na cewa zaben yana da inganci kuma an yi shi cikin adalci.