ICC : Dan Jihadi, Zai Biya Diyya A Timbuktu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23268-icc_dan_jihadi_zai_biya_diyya_a_timbuktu
Kotun hukunta mayan laifuka ta duniya cewa da ICC, ta ce dan jihadin nan na Mali Ahmad al Faqi al Mahdi zai biyan diyya ta Yuro miliyan biyu da dubu dari bakwaiu saboda lalata wurare masu tarihi a birnin Timbuktu.
(last modified 2018-08-22T11:30:33+00:00 )
Aug 17, 2017 10:31 UTC
  • ICC : Dan Jihadi, Zai Biya Diyya A Timbuktu

Kotun hukunta mayan laifuka ta duniya cewa da ICC, ta ce dan jihadin nan na Mali Ahmad al Faqi al Mahdi zai biyan diyya ta Yuro miliyan biyu da dubu dari bakwaiu saboda lalata wurare masu tarihi a birnin Timbuktu.

Kotun dake zama a birrnin hage ta ce al Faqi wanda aka samu da laifin zai biyya wanna diyya ga al'ummar Timbuktu, a cewar alkali Raul Cano.

A watan Satumba bara ne kotun ta yanke ma dan jihadin mai suna Ahmad al Faqi al Mahdi hukuncin dauri na shekara tara, saboda samunsa da laifin jagorantar hari kan masallacin Sidi Yahia da kuma wasu wurare masu tarihi guda tara a Timbuktu dake karkashin kulawar hukumar kula da wurare masu tarihi na duniya cewa da UNESCO.

Al Faqi dai ya kasance mamba a kungiyar Ansar Dine dake da alaka da kungiyar Al'Qaida data kauci ikonn arewacin Mali na tsawan watanni goma a cikinm shekara 2012.