Senegal : Yakin neman zaben raba-gardama kan kundin tsarin mulki
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2329-senegal_yakin_neman_zaben_raba_gardama_kan_kundin_tsarin_mulki
A cikin daren wannan Asabar ne daga misalin karfe 12 na dare ake bude yakin neman zaben raba gardama a game da sabon kundin tsarin mulki a Senegal, wanda shugaban kasar Macky Sall ya gabatar na rage wa'adin mulki daga shekara bakwai zuwa biyar.
(last modified 2018-08-22T06:57:58+00:00 )
Mar 12, 2016 14:30 UTC
  • Shugaba Macky Sall na Senegal
    Shugaba Macky Sall na Senegal

A cikin daren wannan Asabar ne daga misalin karfe 12 na dare ake bude yakin neman zaben raba gardama a game da sabon kundin tsarin mulki a Senegal, wanda shugaban kasar Macky Sall ya gabatar na rage wa'adin mulki daga shekara bakwai zuwa biyar.

Za'a dai shafe mako guda tsakanin masu goyan bayan sauyin da kuma masu adawa da hakan, yayin da sojoji da kuma sauran masu sanye da kaki soji ke jefa kuri’unsu gobe lahadi, yayin da sauran al’ummar kasar sama da milyan 5 za su jefa nasu kuri’un a ranar lahadin makon gobe.

'yan adawa dai da 'yan fara hula a wannan kasa na kira da kada a amunce da rage wa'adin mulkin da shakaru kamar yadda Shugaban kasar Macky Sall ya yi alkawari.

A cikin sabon kundin tsarin mulkin da shugaban Sall ke neman amincewar jama’a, akwai ayoyin doka 15 da ake neman canzawa daga tsohon kundin mulkin kasar.

A nasu bangare mahukuntan kasar ta bakin ministan cikin gida Abdoulaye Daouda Diallo t ace komi ya kammala domin gudanar da zaben yadda ya kamata inda aka zuba sabar kudi da yawan su ya kai biliyan biyu na CFA.