An Tusa Keyar 'Yan Najeriya 135 Daga Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23300-an_tusa_keyar_'yan_najeriya_135_daga_libiya
Mahukuntan Libiya sun tusa keyar 'yan Najeriya 135 zuwa gida karkashin shirin nan na mayar da bakin haure zuwa kasashensu na asali.
(last modified 2018-08-22T07:00:33+00:00 )
Aug 18, 2017 06:30 UTC
  • An Tusa Keyar 'Yan Najeriya 135 Daga Libiya

Mahukuntan Libiya sun tusa keyar 'yan Najeriya 135 zuwa gida karkashin shirin nan na mayar da bakin haure zuwa kasashensu na asali.

Wani jami'in hukumar shigi da fice a Tripoli ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, bakin hauren mata da kananan yara, an ceto su ne a tekun bahar Rum, a kokarin da suke yi na tsallakawa kasashen Turai.

An dai gudanar da aikin tusa keyar bakin hauren ne tare da hadin gwiwar kungiyar kula da kaurar jama'a da duniya cewa HCR domin mayar da bakin hauren zuwa kasashensu na asali.

Lamarin kwarar bakin haure 'yan Afrika zuwa turai dai ya kazanta tun bayan kifar da gwamnatin mirigayi Kanal Gaddafi a cikin shekara 2011.