Nakiya Ta Kashe Sojojin Burkina Faso Uku
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23302-nakiya_ta_kashe_sojojin_burkina_faso_uku
Rahotanni daga Burkina faso na cewa sojojin kasar uku ne suka rasa rayukansu a yayin da motarsu ta taka nakiya a lardin Turonata dake karamar hukumar Tongomayel dake yankin Sahel a arewacin Wagadugu babban birnin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:33+00:00 )
Aug 18, 2017 06:48 UTC
  • Nakiya Ta Kashe Sojojin Burkina Faso Uku

Rahotanni daga Burkina faso na cewa sojojin kasar uku ne suka rasa rayukansu a yayin da motarsu ta taka nakiya a lardin Turonata dake karamar hukumar Tongomayel dake yankin Sahel a arewacin Wagadugu babban birnin kasar.

Sojojin da suka gamu da ajalinsu a wannan lamarin sun hada da maza biyu da kuma macce guda, a cewar kamfanin dilancin labaren Burkina faso na (AIB).

Yankin arewacin Burkina Faso dai ya jima yana fama da hare-haren mayakan jihadi kan jami'an tsaro da kuma fararen hula.

Lamarin dai na zuwa ne kwanaki hudu bayan mumunan harin ta'addancin da ya yi sanadin mutuwar mutane 18 a wani gidan sayar da abunci na Turkawa dake tsakiyar birnin Wagadugu.