An Bude Tashar Talabijin Ta Farko Ta Musulmi A Kenya
An bude tashar talabijin ta farko mallakin musulmi a kasar Kenya wadda za ta rika gabatar da shirye-shirye na addinin muslunci.
Shafin yada labarai na The Star ya bayar da rahoton cewa, an baiwa wannan tashar talabijin taken "fitila ga al’umma" wadda za ta rika yin bayani a cikin shirye-shiryenta a kan addinin muslunci da kuma sauran shirye-shirye da suka shafi al’ummar kasar baki daya.
Usman Warfa shi ne limamin babban masallacin Nairobi, a lokacin da yake gabatar da jawabi a yayin bude wannan tasha ya bayyana cewa, za su yi amfani da wanan dama domin bayyana ma mutane hakikanin addinin muslunci da kuma koyarwarsa, domin kawar da sabanin fahimta da kuma mummunan kallo da ake yi wa addinin musulunci.
Wannan tasha tana a matsayin tashar addini ta uku da aka bude a kasar, bayan manyan tashoshi guda biyu na mabiya addinin kirista, wato tashar GBS da kuma Family TV, wadanda suke gabatar da shirinsu na addinin kirista.