Aljeriya Ta Kara Daukar Kwararan Matakan Tsaro A Kan Iyakokinta
Gwamnatin kasar Aljeriya ta kara tsanata tsaro a kan iyakokinta da kasashen da ke makwaftaka da ita, da nufin ganin ta dakushe yunkurin 'yan ta'adda na kutsa kai a cikin kasarta.
Majiyoyin tsaro a kasar ta Aljeriya sun tabbatar da cewa, wannan mataki ya biyo bayan hare-haren ta'addancin da aka a kan sansanin dakarun majalisar dinkin duniya a kasar Mali, da kuma harin da aka kai a Burkina Faso ne.
majiyoyin sun ce yanzu haka sojojin Aljeriya da dama ne aka aike da su zuwa kan iyakokin kasar da Mali, Nijar da kuma Libya, wadanda tsawon iyakar ya haura kilo mita 2400.
A makon da ya gabata ne manyan jami'an tsaro na kasashen yankin suka gudanar da zama a birnin Nouakchott na kasar Mauritania, domin daukar matakai na hadin gwiwa a kan iyakokinsu, domin tunkarar barazanar tsaro.