Mali : An Jingine Shirin Zaben Jin Ra'ayin Al'umma
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23332-mali_an_jingine_shirin_zaben_jin_ra'ayin_al'umma
Shugaban Ibrahim Bubakar Keita na Mali na sanar da dage shirin zaben jin ra'ayin al'ummar kasar kan yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.
(last modified 2018-08-22T07:00:34+00:00 )
Aug 19, 2017 06:39 UTC
  • Mali : An Jingine Shirin Zaben Jin Ra'ayin Al'umma

Shugaban Ibrahim Bubakar Keita na Mali na sanar da dage shirin zaben jin ra'ayin al'ummar kasar kan yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.

A wani jawabinsa ga al'ummar kasar a cikin daren jiya Juma'a, shugaban kasar ta Mali ya ce an dakatar da shirin zaben na raba gardama kan yiwa sabon kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska.

An dai jingine batun zaben har zuwa wani lokaci da ba'a bayyana ba, a cewar shugaban wanda ya ce babu abunda ba za'a iya yi ba saboda kasarsa musamen kan hada kan al'umma da kuma kaucewa tarzoma.

A kwanan baya dai 'yan adawa da wasu kungiyoyin fara hula sun sha gudanar da zanga-zanga ta nuna kiyaya ga shirin gwamnatin kasar na zaben jin ra'ayin al'umma.