Sharhi:Kokarin HKI Na Samun Gindin Zama A Nahiyar Afirka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i23344-sharhi_kokarin_hki_na_samun_gindin_zama_a_nahiyar_afirka
A kokarinta na fita daga cikin halin kadaici, haramcecciyar kasar Isra'ila na kokarin fadada alakarta da kasashen nahiyar Afirka, dangane da wannan batu, magabatan birnin tel-aviv suka kudiri shirya wani taro mai taken zaman kasashen Afirka da Isra'ila cikin watan OKtoba mai zuwa a kasar Togo.
(last modified 2018-08-22T07:00:34+00:00 )
Aug 20, 2017 00:52 UTC
  • Sharhi:Kokarin HKI Na Samun Gindin Zama A Nahiyar Afirka

A kokarinta na fita daga cikin halin kadaici, haramcecciyar kasar Isra'ila na kokarin fadada alakarta da kasashen nahiyar Afirka, dangane da wannan batu, magabatan birnin tel-aviv suka kudiri shirya wani taro mai taken zaman kasashen Afirka da Isra'ila cikin watan OKtoba mai zuwa a kasar Togo.

A yayin da haramcecciyar kasar Isra'ila ke fuskantar suka daga magabatan kasashe daban daban na duniya a game da bakar siyasar tsokana da kuma fice gona da iri a kan al'ummar Palstinu, a yanzu magabatan birnin Tel-Aviv sun mayar da hankulan su zuwa kasashen nahiyar afirka. ko da yake, shekaru da dama da suka gabata, wasu daga cikin shugabanin HKI sun bunkasa alakar da su da fagen siyasa da tattalin arziki a wasu kasashe na Afirka da nufin cimma manufofinsu, to amma hakan, bai kai ga cimma manufar da magabatan HKI ke so ba,domin haka mahukuntan HKI cikin wata sabuwar mahanga suka sake daukan sabuwar siyasa a kokarin cimma manufofinsu a nahiyar Afirka, ziyarar da wasu magabatan HKI suka kai a wasu kasashen nahiyar Afirka da kuma halartar taron kungiyar kasashen Afirka na daga ciki wannan kudiri.

Nahiyar Afirka dai nada mahimanci ga HKI a bangare mababbanta, kama daga bangaren siyasa, Soja, tsaro da tattalin arziki, shekaru da dama magabatan HKI suke yi na kokarin kula alaka da kasashen Afirka domin amfani da matsayinsu, musaman ma kuri'arsu na taron kasa da kasa a MDD. har ila yau domin magance matsalar rashin amincewar da wasu kasashe suka yi tare kuma da hana kafa kungiyoyi masu adawa da haramcecciyar kasar a nahiyar Afirka.

A kwanakin baya, Firaministan HKI Benjamin Netanyahu ya bukaci jakadun HK da su  canya siyasar su ta yadda za su samu kuri'un kasashen Nahiyar Afirka da wasu kungiyoyin kasa da kasa a Majalisar dinkin Duniya.

A bangaren tattalin arziki, kasashen Afirka na da dunbun arziki na karkashin kasa da Al'umma, to amma saboda bakar siyasar kasashen milkin mallaka da kuma rashin takaici na dama daga cikin  shugabanin kasashen Afirkan, har yanzu wasu kasashen na fama da bakin talauci da kuma rashin ci gaba  na bangarori daban daban. matsalar tattalin arzikin da kasashe Afirkan ke fama da shi shi ya sanya magabatan HKI suka yi amfani da wannan dama domin cimma manufofinsu a nahiyar, inda a halin da ake ciki, suka yi alkawarin bawa kasashen taimakon kudade, tare kuma da mayar da bangaren fusahar su zuwa nahiyar, wannan alkawari na taimakon da mahukuntar HKI suke yi nahiyar Afirka na zuwa ne a yayin da rahotanni ke cewa HKI na fuskantar matsalar tattalin arziki, inda take neman taimakon kudade daga kasar Amurka da kuma kungiyar kasashen Turai, tare da bukatar bashi na tsahon lokaci.

Duk da kokarin da mahukuntar HKI ke yi na fadada alakarsu da Nahiyar Afirka, to amma da dama daga cikin kasashen da suka jima cikin tunanin samun cikekken 'yanci da kuma suka san hakikanin manufar HKI ba za su amince da wannan sabon milkin mallaka ba, domin da dama daga cikin al'ummar kasashen Afirka na adawa da kisan kiyashi da kuma mamayar da HKI ke yi wa al'ummar Palastinu.a cewar Jakadan kasar Afirka ta kudu a Labnon, kudirin HKI ba wani abu ba ne face mumunar amfani da kuma yaudawa domin sauya  tunanin al'ummar Afirka game da ta'addancin da suke yi a kan al'ummar Palastinu.

Masu sharhi game da harakokin yau da kulun na ganin cewa wannan shiri na mahukuntan HKI ba zai kai ko ina ba, saboda kyakkyawan sanin da al'ummar Afirka suka yiwa HKI ba a shirye suke, su amince da siyasa da kuma kula alaka da magabatan birnin Tel-Aviv ba.