Afirka Ta Kudu Ta Amince Da Bukatar Uwar Gidan Shugaban Kasar Zimbabwe
Uwargidan shugaban kasar Zimbabwe, Grace Mugabe, taki halartar taron matan shugabannin kasashen yankin kudancin Africa ba, wanda aka fara shi a wannan Asabar, bayan da ta ki amsa kiran jami'an 'yan sanadar kasar Afirka ta kudu.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a jiya Assabar gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta amince da bukatar uwar gidan shugaban kasar Zimbabwe Grace Mugabe na bata mafukar siyasa tare da bata izinin komawa kasar ta.
A makun da ya gabata ne, aka zarki Uwargidan shugaban kasar Zimbabwe, Grace Mugabe da cin zarfin wata mata mai suna Gabriella Angelsa 'yar shekaru 22 a wani Otel ta hanyar yi mata duka a kai, wanda hakan ya sabbaba wa matar samun rauni a kai.
Mista Grace ta aikata wannan danyan aiki ne bayan da ta yi shakku game da alakar dake tsakanin Matar da 'ya'yanta.
Domin amsa tuhumar da ake yi mata, hukumar 'yan sanda tagayyaci uwargidan shugaban kasar ta zimbabwe Grace mugabe mai shekaru 52 a Duniya, to saidai Grace ba ta ki amsa kiran, lamarin da ya sanya suka bayar da umarnin hanata fita daga cikin kasar.
Gwamnatin kasar Zimbabwe ta bukaci gwamnatin Afirka ta kudu da su bawa uwargidan shugaban kasar kasar mafuka, bayan dogon nazari, a jiya assabar gwamnatin ta amince da bukatar.