Sudan: Jam'iyyun Siyasar Kasashen Afirka Sun Yi Taro A Birnin Khartum.
Wakilan jam'iyyun siyasa 32 ne da su ka fito daga kasashen Afirka daban-daban su ka yi taron domin karfafa alakar aiki a tsakaninsu.
Pira ministan kasar Sudan, Bakri Hassan Salih ya shaidawa kamfanin dillancin labarun Anatoli cewa; Taron wanda yake da taken : Taro na uku na jam'iyyun siyasar Afirka' an yi ne domin karfafa alakar aiki a tsakanin kasashen na Afirka.
Hassan Saleh ya kuma kira yi mahalarta taron da su kare kasashensu daga sabon mulkin mallaka na kasashen turai.
Shugaban majalisar jam'iyyun siyasar nahiyar Afirka Dayis Moyla ya ce; An yi taron ne saboda tattauna mawuyacin yanayin siyasa da aka shiga a nahiyar, haka nan kuma yake-yaken cikin gida da ake fama da su.
A shekarar 2013 ne aka kafa majalisar jam'iyyun siyasar Afirka da zummar karfafa alakar aiki a tsakanin kasashen.