Sojojin Nijar Sun Hallaka 'Yan Boko Haram 40
Aug 22, 2017 10:56 UTC
Rundinar sojin Nijar ta sanar da cewa dakarunta sun hallaka 'yan ta'adda na boko haram kimanin 40 a yankin Barwa dake arewa maso yammacin jihar Diffa.
Saidai a cikin sanarwar da ta fitar rundinar ta ce ta rasa sojinta guda sakamakon raunukan da ya samu a yayin gwabza fada da 'yan ta'addan.
A ranar 19 zuwa 20 ga watan nan ne dakarun sojin kasar ta Nijar cewa da (FDS) suka kaddamar da wani gagarimin farmaki kan 'yan ta'addan na Boko Haram
A wani jawabinsa na jajibirin ranar samun yancin kai ta kasar, Shugaba Isufu Mahamadu ya umurci dakarun kasar dasu yi duk iya kokarinsu wajen kubutar da mata da yaran nan su guda 39 da kungiyar ta Boko Haram ta sace a jihar Diffa cikin watan Yulin da ya gabata.
Tags