Ana Dakon Sakamakon Zaben Shugaban Kasa A Angola
Al'umma a Angola na ci gaba da dakon sakamakon zaben shugaban kasar da aka kada kuri'asa a jiya Laraba.
A wannan Alhamis ce ake sa ran hukumar zaben kasar za ta fara bayyana sakamakon farko-farko na zaben wanda zai kawo karshen mulkin shekaru 38 na shugaba Jose Eduardo dos Santos.
Kafin hakan dai wani hasashen da akeyi ya nuna cewa jam'iyyar MPLA dake shugabancin kasar tun 1975 ce zata samu gagarimun rinjaye a majalisar dokokin kasar.
Hukumar zaben kasar dai ta Angola, ta ce ta jirkita kada kuri'a a rumfuna 15 dake sassa daban-daban na kasar har zuwa ranar 26 ga wata.
Mai Magana da yawun hukumar zaben kasar Julia Ferreira ta bayyana cewa, baki daya aikin kada kuri'ar ya gudana lami lafiya, sai dai kuma wasu matsaloli kamar rashin kyan yanayi sun kawo cikas ga aikin kai na'urorin kada kuri'a zuwa yankuna masu wahalar shiga a larduna uku na kasar wato, Luanda-Norte,da Moxico da lardin Bengula.
Tun kafin zaben dai mayan jam'iyyun adawa na kasar sun koka da abunda suka kira rashin tsari da adalci a babban zaben.